Labarai
Cunkuson mutane a cibiyoyin samar da katin dan kasa a Kano bakon al’amari ne – NIMC
Hukumar samar da lambar katin dan kasa a nan Kano ta ce, cunkoson al’umma da ake samu a cibiyoyin samar da katin dan kasa a jihar Kano a kwanakin nan, bakon lamari ne da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan da aka samar da hukumar.
Daraktan kula da hukumar shiyyar Kano Alhaji Lawal Yahaya ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi “na nan tashar Freedom Radio da shirin ya mayar da hankali kan yadda ake samun cunkoson mutane a wajan yin rajistar a kwanakin nan.
Ya ce, cunkoson na da alaka da yadda gwamnatin tarayya tayi barazanar kulle layukan wayar da basu hade layin nasu da lambar katin dan kasa ba, wanda hakan ya sanya jama’a suka bazama domin mallakar katin a yanzu.
Alhaji Lawan Yahaya ya ce, cunkoson jama’ar na barazana ga lafiyarsu baya ga rashin wadatattun kayan aiki a hukumar wanda ke kara ta’azzara cunkoson.
You must be logged in to post a comment Login