Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalilan da ya sanya za’a fara yi wa makaraban gwamnati allurar riga kafin Corona

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo har ma da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne za a fara yiwa allurar riga kafin cutar corona tare da watsa shi kai tsaye ta gidan talabijin.

Babban darakta na hukumar kula da asibitocin lafiya matakin farko Dakta Faisal Shu’aibu ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da yake jawabi ga kwamitin yaki da cutar corona na gwamnatin tarayya.

Ya ce, shugabannin hadi da wasu sanannun mutane a Najeriya ne za su fara karbar rigakafin cutar don ya zamo fadakarwa ga al’umma ga me da mahimmancin karbar rigakafin.

Dakta Faisal Shu’aibu ya bukaci ‘yan Najeriya da su tabbatar sun karbi rigakafin da hannu bibbiyu tare da bada hadin kai don yaki da cutar corona a Najeriyar.

Idan dai za a iya tunawa Najeriya na tsammanin karbar allurar rigakafin kimanin miliyan arba’in da biyu a shekarar da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!