Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar Kwastam ta cafke mota maƙare da Sabulan wanka

Published

on

Hukumar hana fasa ƙauri ta ƙasa Custom ta tabbatar da kama wata motar tirela dauke da sabulu GIV da ake zargin an shigo da shi ƙasar Najeriya ba bisa ƙaƙi da ba.

Shugaban hukumar da yake kula da yankin bodojin Arewa maso Yamma Controller kolapo Oladeji ne ya tabbatar da hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishin hukumar dake Hajj Camp a jihar Kano.

Oladeji ya kuma ce wannan sabulun da aka kama sabulu na wasu ƙasashen kuma aka shigo da shi Najeriya la’akari da yadda bodojin ƙasar suke a kulle.

Haka kuma wannan kayan an sami masaniyar an shigo da su ƙasar nan a ƙananan ababan hawa aka tara su a wata makaranta mai suna Ɗalladi Firamare school dake ƙaramar hukumar Gumel a Jihar Jigawa.

kana daga bisa ni aka zuba a babbar mota zuwa inda za’a kai su domin cefanar da su.

Kolapo Oladeji ya kuma ce zasu ci gaba da sanya ido kan duk wa’inda aka samu da fasa ƙaurin kayan zuwa ƙasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!