Labaran Kano
Cutar ciwon kunne na raguwa sakamon wayar da kan al’umma- Likita
Wani Kwararren likitan kunne da hanci da kuma makogwaro Dakta Ado Hamza Soron Dinki ya bayyana cewa lalurar kunne na daya daga cikin cutar da ke wahalar da mutane, wanda idan har ya yi kamari ya kan haifar da matsalar rashin ji.
Dakta Ado Hamza Soron Dinki, da ke aiki a asibitin kwararru na Muhammdu Abdullahi Wase ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan gidan Rediyon Freedom, wanda ya mayar da hankali kar ranar lalurar ji ta duniya da majalisar dinkin duniya ta ware wadda ake gudanarwa a yau.
Likitan ya kara da cewar an samu raguwar lalurar sakamakon wayar da kan al’umma da ake gudanarwa game da lalurar da ji tare da matsalolin da take haifarwa.
Dakta Ado Hamza ya ja hankalin iyaye cewa da zarar sun ji yaransu na koke- koke tare da shafa kunnensu, to su hanzarta kai su asibiti don duba lafiyarsu, inda ya yi kira ga al’umma kada su bari wani ya duba lafiyarsu matukar ba likitan kunne bane don gujewa afkuwar matsala.
You must be logged in to post a comment Login