Labarai
Cutar Deptheria ta kama mutane 557, tare da kashe 73 a Nijeriya- WHO
Rahoton WHO ya nuna an samu ɓarkewar cutar Deptheria a jihohi 21
An fi samun yawan alkaluman waɗanda suka kamu da cutar ce a Kano
Daga ranar 14 ga watan Mayun bara zuwa 9 ga watan Afrilun bana lamarin ya fi kamari
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce, cutar mashaƙo watau Deptheria, ta kashe kimanin mutane 73 yayin da wasu kuma karin 557 suka kamu da cutar tun a farkon shekarar bana.
Hakan na cikin wani rahoto da hukumar ta fitar jiya Laraba, inda ta ce, an samu ɓarkewar cutar a jihohi 21 na Nijeriya.
A cewar WHO, an fi samun yawan alkaluman waɗanda suka kamu da cutar ce a jihar Kano, inda mutane dubu 1,118 suka kamu da ita.
Sai kuma jihar Yobe mai mutane 97 da Katsina mai mutane 61 da suka kamu, jihar Legas na da mutane 25 sai Sokoto mai mutane 14 da kuma Zamfara da aka samu mutane 13 da suka kamu da cutar.
Rahoton ya kuma ce, daga ranar 14 ga watan Mayun bara 2022 zuwa 9 ga watan Afrilun bana an samu alkaluman mutane dubu 1,439 da ake zargin sun kamu da cutar ta mashaƙo, inda cutar ta yi sanadiyyar rayuka 73.
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login