Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da ɗumi-ɗumi: Ƴan ƙwadago sun jingine shiga yajin aiki

Published

on

Gwamnatin tarayya da ƴan ƙwadago sun cimma yarjejeniya dangane da yunƙurin da ƴan ƙwadagon suka yi na shiga yajin aiki daga yau Litinin.

Ƙaramin ministan ƙwadago na ƙasa Festos Keyamo ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce, gwamnatin tarayya ta janye ƙarin farashin lantarki har zuwa nan da makonni biyu masu zuwa.

Sakamakon yarjejeniyar da aka cimma, ƙungiyoyin ƙwadagon sun dakatar da shirin su na tsunduma yajin aikin daga yau.

Cikakken bayanin zai zo a nan gaba kaɗan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!