Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da ɗumi-ɗumi: Ganduje ya sauke Baba Impossible

Published

on


Gwamnan ya kuma maye gurbinsa da DaktaNazifi Bichi.

An sauke Baba Impossible ɗin ne biyo bayan halin rashin ɗa’a da ya nuna da kuma furta wasu kalamai a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati mai riƙe da muƙami.

Kwamishinan yaɗa labarai Malam Muhammad Garba ya sanar da korar Baba Impossible a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Asabar, 31 ga watn Disamba.

Sanarwar ta ce, an samu Baba Impossible da laifin gudanar da al’amuran ofishinsa a matsayin sana’a na ƙashin kansa, har ma ya kan rage kwanakin zuwa aiki ga ma’aikatansa.

Cikin ranakun da ya ragewa ma’aikatansa sun hada da ranakun Laraba da Juma’a.

Kwamishinan ya kara da cewa baya ga gudanar da aiki ba tare da tuntubar juna ba, Baba Impossible baya biyayya ga gwamnati.

Ya kuma kara da cewa tuni Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aika wa majalisar dokokin jihar sunan wanda aka zaɓa da zai maye gurbinsu wato Dakta Nazifi Ishaq Bichi na Jami’ar Bayero Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!