Addini
Da ɗumi-ɗumi: An ceto masu sallar Tahajjud 30 da ƴan bindiga suka sace a Katsina
Wata hadakar jami’an tsaro na haɗin gwiwa tsaƙanin ƴan sanda sojoji da sauran jami’an tsaro na sa kai, sun samu nasarar ceto mutane 30 wadanda ƴan bindiga suka sace su lokacin da suke tsaka da sallar tahajjud.
Tun farko dai ƴan bindigar sun sace mutanen 40 ne wadanda ke tsaka da sallar tahajjud kafin daga bisani jami’an tsaro su ceto 30 daga cikinsu.
Ya ce ƴan bindigar da ke da yawan gaske sun fito ne daga wani daji da ke garin Zurumi wani gari da ke kan iyaka da jihar Zamfara inda suka sace mutanen da ke tsaka da sallah.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa ya tabbatar da sace mutanen tare da sake su.
A cewar SP Gambo Isa ƴan bindigar sun kewaye masallatan ne da ke sallah a wani sabon masallaci da ke garin Jibiya inda daga nan ne kuma suka sace su.
You must be logged in to post a comment Login