Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Ganduje ya gabatar da sama da Biliyan 245 a matsayin daftarin kasafin 2023
Da safiyar ranar Juma’a ne gwamnan Kano Daka Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da sama da Naira Biliyan 245 a matsayin daftarin kasafin 2023 ga majalisar dokoki.
Da yake gabatar da kasafin, gwamnan ya ce a baɗi gwamnatinsa za ta mayar da hankali a ɓangaren bada ilimi kyauta kuma dole.
Sannan za a gyara tsarin almajiranci da tabbatar da tsaro da kuma koyawa matasa sana’o’i.
Baya ga wannan ma, kasafin zai mayar da hankali wajen inganta ɓangaren lafiya da wasu sauran muhimman ɓangarori.
Tun da fari gwamna Ganduje ya fara da tulawar ayyukan da gwamnatinsa ta samu nasarar kammalawa a bana kamar yadda ya kuduri aniya a cikin kasafin kudin bara da ya gabatarwa majalisar da yawan su ya kai Naira Biliyan 196.
Cikin ayyukan da gwamnan ya lissafo sun haɗa da aikin sanya kyamarorin tsaro a sassa da dama na jihar, da aikin titin ƙarƙashin ƙasa na Ƙofar Ruwa.
Sai Gadar sama ta shiekh Ƙariballah Nasir Kabara wadda ke daura da asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da Gadar Muhammadu Buhari da ke Hotoro da gina cibiyar koya sana’o’i ta Aliko Dangote da sauran su.
Kamar yadda wakilin Freedom Radio Auwal Hassan Fagge ya rawaito.
You must be logged in to post a comment Login