Labarai
Da dumi dumi: Gwamna Alia na Benue ya rushe Majalisar zartaswar jihar

Gwamna Alia na Jihar Benue ya rusa Majalisar Zartaswar Jihar tare da umurtar kwamishinoni da su mika ragamar mulki ga sakatarorin dindindin na ma’aikatunsu.
Cikin wani bayani da mai magana da yawun gwamnan, Tersoo Kula ya fitar, ya nuna cewa gwamnan ne da kansa ya sanar da wannan mataki a ƙarshen taron majalisar zartarwa ta jihar Benue na karo na 12 a shekarar 2025.
Gwamna ya nuna godiyarsa ga dukkan tsofaffin kwamishinonin da suka yi aiki tare da shi na tsawon shekaru biyu, yana mai kiraye-kiraye ga wadanda ba za a sake naɗa su ba ko kuma ba za a kira su ba, da su ci gaba da kasancewa cikin jam’iyya da haɗin gwiwa da tsarin, domin dai kawai suna ba wasu ‘yan kasa damar su ma su samu zarafin bada gudunmawarsu.
Ya ƙara da cewa, rushewar bata shafi Shugaban Ma’aikata na jihar ba ta shafi kwamishinoni ne kawai.
Da yake magana a madadin sauran kwamishinonin da aka rushe, Barista Bemsen Mnyim, ya godewa gwamna saboda damar da ya ba su na yin hidima ga jihar.
You must be logged in to post a comment Login