Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Kotu ta yanke wa makashin Ummita hukuncin Rataya
Babbar kotun jahar Kano mai lamba 16 karkashin jagorancin mai sharia Sanusi Ado ma’aji, ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya akan mutumin nan dan kasar China Frank Genk Quarong bayan ta same shi da laifin kisan kai.
Mai shari’a Sanusi ma’aji ya yi umarnin a rataye Genk har sai rai yayi halinsa bisa samunsa da laifin kashe matashiyar nan Ummita Buhari.
Andai samu Genk da laifi sakamakon shaidun da masu kara suka gabatar wadanda suka tabbatarwa da kotun cewar wanda ake tuhumar ya aikata laifin kisan kai akan wata matashiya mai suna Ummita wadda shaidun suka bayyanawa korun cewar Frank Genk ya hallaka ta a ranar 16 ga watan Satumba na shekarar 2022 da misalin karfe 9 na dare.
Kotun ta gamsu da shaidun masu gabatar da kara guda 6 yayin da tayi watsi da shaidar kariya bisa rashin hujjoji.
Gabannin zartas da hukuncin lauyan dan china barrister Muhammad Dan,azumi ya roki kotun da ta yiwa dan chinan afuwa a karkashin sashi na 113 na ACJL sai dai kotun ta bayyana cewar wannan hurumin gwamnati ne.
Jawaban kariya da Genk Frank ya yi a kotun sun yi nuni da cewar akwai soyayya tsakanin shi da marigayiya Ummita.
Rahoton: Aminu Abdu Bakanoma
You must be logged in to post a comment Login