Labarai
Da ɗumi-ɗumi- Lauyoyin Abduljabbar sun janye daga ci gaba da bashi kariy
Lauyoyin Malam Abduljabbar sun janye daga bashi kariya a gaban kotun shari’ar musulunci a Alhamis ɗin nan.
Lauyoyin sun janye ne jim kaɗan bayan gabatar da takardar gwajin asibitin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma shaidar gwajin lafiyar kunne da aka yi masa kuma suka nuna lafiyar sa ƙalau.
Bayan gabatar da takardar ɗaya daga cikin lauyoyin da ke kare Malamin Barista Haruna Magashi ya bayyanawa Kotu cewar sun janye kariyar da suke ba shi.
Wannan dai ya biyo bayan ci gaba da sauraron ƙarar da ake tsakanin Malam Abduljabbar Kabara da gwamnatin Kano, wanda kotun shariar musulunci da ke zamanta a ƙofar kudu karƙashin mai shari’a Ibrahim Sarki ta sake zama don ci gaba da sauraren karar.
Kotu ta bada umarnin aikewa da abduljabbar Kabara asibitin Dawanau
Daga karshe Kotu ta tambayi Malamin cewar ko yana da sha’awa ɗaukar wani lauyan? Sai ya ce ƙwarai kuwa, kotun kuwa ta amince.
Sai dai an kuma ɗage zaman kotun zuwa ranar 30 ga watan domin ci gaba da sauraran ƙarar.
A zantawar wakilinmu Aminu Abdu Baka Noma da lauyan gwamnati Mamman Lawan Yusufari ya yi ƙarin haske, inda ya ce “Bayan an gabatar da sakamakon lafiyar malamin kuma ya tabbatar da cewa bashi da matsala, lauyoyin sa sun janye a don haka mu ba mu da hurumin yin suka tun da doka ta bai wa lauyoyi damar su janye a duk sanda suke so, shi kuma an bashi dama ya kawo wasu lauyoyin”
Shi ma lauyan da ya janye daga shari’ar ya yi karin bayani inda ya ce” mun tattauna da wanda ake kara mun samu matsaya kan cewa janyewar mu ita ce masalaha a wannan shari’ar, a don haka ba za mu fito mu bayyana dalilin mu ba ko kuma abin da muka tattauna, inda ya musanta cewa ba wata barazana da ta sa suka janye”.
Tuni dai jami’an gidan gyaran hali sun sake wucewa da malam Abduljabar gidan gyaran halin kamar yadda kotu ta ba su umarni.
You must be logged in to post a comment Login