Labarai
Da ɗumi-ɗumi:Buhari zai naɗa sabon minista

Shugaban ƙasa Muhammdu Buhari ya miƙa sunan Mu’azu Jaji Sambo daga jihar Taraba gaban majalisar dattijai domin naɗa shi a matsayin sabon minista.
Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan lokacin da yake karanto wata takarda da shugaban ya rubutawa zauren a ranar Talata.
Shugaba Buhari ya buƙaci majalisar dattawa da ta tantance tare da tabbatar da Ma’azu Jaji domin naɗa shi a matsayin sabon minista.
You must be logged in to post a comment Login