Labarai
Da dumi-dumi : Ganduje ya aikewa majalisa takardar gabatar da kudirin kasafin kudi
Gwamnatin Kano ta aikawa majalisar dokoki ta jihar Kano takardar neman sahalewar ta wajen gabatar da kudirin kasafin kudin badi a gobe Talata.
Tun a ‘yan kwanakin da suka gabata ne Gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje a ya yin zaman majalisar zartarwa ta jiha ya bayyana cewar gwamnati zata gabatar da kudirin kasafin kudin badi a yau Litinin 26 ga watan Okotoba.
Sai dai a ya yin zaman majalisar dokokin ta Kano da safiyar yau ta bayyana cewar gwamnatin Kano ta aikemata da takardar neman sahalewar gabatar da kudirin kasafin kudin badi a gobe Talata.
Shugaban majalisar dokoki ta Kano Abdul’aziz Garba Gafasa ne ya karanta takadar a kwaryar majalisar ya yin zaman da take yi a halin yanzu.
You must be logged in to post a comment Login