Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

El- Rufa’i ya yi tir da fasa rumbun adana kayayyakin tallafi a Kaduna

Published

on

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi tir da fasa rumbun adana kayayyakin tallafin rage radadin corona da wasu mutane suka yi a Jihar, inda ta ce za ta binciko mutanen tare da daukar matakin da ya dace a kansu.

Mataimakiyar gwamnan jihar Dakta Hadiza Balarabe ce ta bayyana hakan yayin da take hira da manema labarai a daren jiya a Kaduna.

Hadiza Balarabe ta ce tuni jami’an tsaro suka cafke wasu daga cikin wadanda suka yi aika-aikar inda ta ce za a iya kiransu da barayi, kasancewar sun dauki kayan da ya kamata a rabawa al’umma.

Ta kuma gargadi wadanda suka dauki kayan da kada su yi amfani da su, kasancewar wa’adin amfani da mafi yawa daga cikinsu ya kare, a don haka suna iya haifar da illa ga lafiyar bil’adama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!