Labarai
Da Dumi-dumi: Gwamnatin Kano ta maka Ganduje da matarsa da wasu mutane 6 a Kotu kan zargin almundahanar kudade
Gwamnatin jihar Kano, ta maka tsohon gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsat Umar da kuma dansa Umar Abdullahi Umar da karin wasu mutane 5 a gaban kotu bisa tuhumetuhume guda 8 masu alaka da cin hanci da rashawa da almundahana da kuma yin sama da fadi da wasu makudan kudade.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne ta cikin wata takardar shigar da kara mai dauke da kwanan watan 3 ga wannan watan da muke ciki na Afrilu wadda kuma ke dauke da sunan shaidu kan karar.
Wadanda ake karar sun hada da Abdullahi Umar Ganduje da Hafsat Umar da Abubakar Bawuro da Umar Abdullahi Umar da Jibrilla Muhammad sai Lamash Properties Ltd da Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises.
You must be logged in to post a comment Login