ilimi
Da gangan gwamnatin tarayya ke yunkurin tunzura mu- ASUU

Kungiyar malaman Jami’oi na Najeriya ASUU, ta ce, da gangan gwamnatin tarayya ta ki biyan bukatun da ta gabatar mata da kuma alkawarin da suka kulla, kuma ta ke san yin amfani da hakan wajen tunzura kungiyar don ta tafi yajin aiki.
Shugaban tsare-tsare na kungiyar da ke yankin Benin da ya kunshi jami’oi 10 Farfesa Monday Igbafen, ne ya bayyana hakan a garin Asaba da ke jihar Delta.
A cewarsa da gangan gwamnati ta ki biyan hakkokin membobinta da kuma kula da makarantu yadda ya kamata.
A domin hakan kungiyar ke bukatar al’ummar Najeriya da su tashi tsaye wajen kula da Jami’oi ba tare da la’akari da gwamnati ba.
You must be logged in to post a comment Login