Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Da kyar nasha : Real Madrid ta doke Chelsea a kofin zakarun turai

Published

on

Zakarun gasar cin kofin  turai Champions League har sau 13 a baya Real Madrid, tayi tashin  nasara a hannun Chelsea da ci 3-2.

An dai gudanar da wasan a filin Santiago Bernabou da ke kasar Spain a ranar Talata 12 ga Afrlin 2022.

Wasan dai shi ne zagaye na biyu na matakin dab dana kusa da karshe wato Quarter Final a gasar ta Champions League.

Inda jumulla gida da waje Real Madrid tayi nasara akan Chelsea da ci 5-4.

Dan wasan Chelsea Mount ne ya fara zura kwallon farko  a minti na (14′), sai Rudiger ya zura ta biyu a minti na (50′)

Yayinda dan wasan kasar Jamus Werner ya kara kwallo ta uku a minti na (74′) bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Daga bangaren Real Madrid kuwa ‘yan wasa irinsu Rodrygo da Benzema ne suka zura kwallayen da ta baiwa tawagarsu nasara a minti na 79 da 95.

A makon da ya gabata dai a filin wasa na Stamford Bridge Chelsea tayi ra shin nasara a hannun Real da ci 3-1.

Jumulla dai Real Madrid tayi nasara da ci 5 da 4 a wasa gida da waje da suka fafata.

A daya wasan da ya gudana a yau Bayern Munich itama ta fice daga gasar bayan rashin nasara da ta yi a hannun Villarreal da ci 2 da 1.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!