Labarai
Da yawa daga cikin iyaye ba su san yadda TIKTOK ke ɓata tarbiyyar yaran su ba – Afakallah
Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano ta buƙaci iyaye da su lura da yadda yaran su ke amfani da wayoyin salula.
Shugaban hukumar Isma’ila Na-Abba Afakallah ne ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi baku cin tawagar ƴan jarida masu gabatar da shirye shiryen al’umma wato magazine News.
Afakallah ya ce “Akwai wani dandali da a yanzu yake ɓata tarbiyyar yara maza da mata wanda ake kira TIKTOK da mafi yawan iyaye ba su san yaran su na amfani da shi ba”.
“Ɗabi’un da yara ke aikatawa a wannan dandali ko kuma suke kalla ba zaka taɓa tunanin ƴaƴan musulmi ba ne” a cewar shugaban hukumar.
Har ma ya ce, lallai ne sai iyaye sun sanya ido kan yadda yaran su ke Amfani da wayoyin hannu don sanin me suke aikatawa ko da a cikin gida.
“Wannan dandali ya zama wajibi a fito a yaƙe shi ba batun hukuma ba ne kaɗai batu ne da ya shafi kowa musamman ma iyaye”.
Isma’ila Na-Abba Afakallah ya buƙaci matasan da su riƙa tunanin rayuwar ta gaba ba iya ta lokacin ƙuruciya ba.
You must be logged in to post a comment Login