Labarai
Dage takunkumi zai habaka tattalin yammacin Afrika- Sanatocin Arewa
Kungiyar Sanatocin Arewa ta yabawa ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta ECOWAS, sakamakon janye jerin takunkuman da ta ƙaƙabawa ƙasashen Nijar Da Burkina Faso, da kuma Mali sakamakon Juyin mulkin da akayi a kasashen.
Wannan na cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun ƙungiyar, kuma sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdruhaman Kawu Sumaila ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta kuma ce janye takunkuman da ECOWAS ta yi wa kasashen ya sake tabbatar da aniyar ƙungiyar na samar da dai-dai to da kuma ciyar da yankin Afrika ta yamma gaba.
A jiya Asabar ne dai ƙungiyar ECOWAS, ta sanar da janye takunkuman da ta ƙaƙabawa ƙasashen Nijar da Burkina Faso da Mali, a taron da tayi a Abuja, da ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yunkuri na sauƙaƙawa Al’ummar ƙasashen ƙuncin rayuwar da suka shiga la’akari da tunkarowar watan Azumin Ramadana.
You must be logged in to post a comment Login