Labarai
Dakarun sojin kasar sun ceto mutane 2 da aka sace tare da kama wasu da ake zargi

Dakarun Rundunar Operation Haɗi Kai sun ceto mutane 2 da aka sace tare da kama wasu da ake zargi da kai wa ‘yan ta’adda kayayyaki a Jihohin Borno da Adamawa.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran rundunar Kaftin Mohammed Goni ya fitar.
Ya ce, dakarun sun kuma daƙile wani hari da mayakan ISWAP suka kai a sansanin soji da ke Logomani a jihar Barno.
Sanarwar ta ce, dakarun rundunar sun kai sumame maboyar ‘yan ta’adda a Karamar Hukumar Askira Uba, ta jihar Borno, inda suka kwato kuɗaɗe da kayan abinci da sauran kayayyakin da ake zargin ana amfani da su wajen tallafa wa ayyukan ‘yan ta’adda.
Rundunar ta ce, dakarun sun kama wasu da ake zargi da samar wa ‘yan ta’adda kayan tallafi a sassan jahohin Borno da Adamawa, tare da kwato bindiga, harsasai, kudi, magunguna, kayan gini da sauran kayayyaki.
You must be logged in to post a comment Login