Labarai
Minista ya yaba wa Gwamnatin Kano kan inganta muhalli

Ministan Muhalli na Najeriya, Balarabe Abbas Lawal, ya yaba wa gwamnatin Jihar Kano bisa matakan da take dauka na dasa bishiyoyi da farfado da muhalli, yana mai cewa jihar ta zama abin koyi wajen yaki da sauyin yanayi.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin Ranar Great Green Wall ta shekarar 2026 da aka gudanar a Kano, inda aka kuma kaddamar da shirin dasa bishiyoyi na shekarar 2026, tare da mika ginin ofis ga Hukumar Kasa mai kula da shirin Great Green Wall.
A jawabinsa, Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya ce mayar da hedikwatar Hukumar Great Green Wall zuwa Kano wani muhimmin ci gaba ne ga kokarin kare muhalli a Najeriya.
Ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da mayar da hedikwatar hukumar zuwa Kano, yana mai cewa hakan zai kara karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar wajen dakile kwararowar hamada da farfado da gurbatattun filaye.
Dakta Hashim ya ce gwamnatin Kano ta samar da manufofin sauyin yanayi tare da inganta matsayinta a fannin gudanar da harkokin sauyin yanayi daga matsayi na 34 a shekarar 2024 zuwa na hudu a shekarar 2025.
Ya kuma bayyana cewa jihar ta dasa bishiyoyi sama da miliyan biyar tare da farfado da fiye da hekta dubu 50 na gurbatattun filaye ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen dasa bishiyoyi, kare kasa daga zaizayar kasa da kuma sauran ayyukan inganta muhalli.
Kwamishinan ya ce sabon shirin SURAGGWA zai taimaka wajen fadada ayyukan farfado da muhalli, bunkasa hanyoyin dogaro da kai da kuma karfafa matakan tinkarar sauyin yanayi a Kano da sauran sassan Arewacin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login