Labarai
Shugaba Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro a fadar mulki ta Villa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci wani taron tsaro a Fadar sa da ke Abuja da yammacin Alhamis din makon nan tare da manyan hafsoshin rundunonin tsaro da shugabannin hukumomin leƙen asiri.
Rahotonni sun bayyana cewa taron ya mayar da hankali ne kan nazarin halin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya, da kuma duba yadda ake gudanar da ayyukan soji a yankunan da ake fama da matsalolin tsaro.
Sai dai majiyoyi sun tabbatar da cewa, an gudanar da taron ne a sirrance har na tsawon fiye da sa’o’i biyu.
Wananan dai na zuwa ne bayan da rundunar Operation FANSAN YAMMA ta sanar da dakile wani shirin hare-haren ‘yan ta’adda a jihohin Zamfara da Katsina.
Rundunar ta ce jiragen yaƙin sojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan ayarin ‘yan ta’adda da ke kan babura, tare da kashe wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga mai suna Alhaji Tukur a yankin Dogon Kade.
Haka kuma, a Arewa maso Gabas, rundunar Operation Hadin Kai ta ce ta dakile wani hari da aka kai sansaninta na Mairari a jihar Borno.
Sai dai har zuwa wannan lokaci, fadar shugaban ƙasa ba ta fitar da wata sanarwa kan sakamakon taron ba.
You must be logged in to post a comment Login