Labarai
Dakile satar amsa ne ya janyo faduwar dalibai a JAMB- Ministan Ilimi

Ministan ilimin na Najeriya Dakta Tunji Alausa, ya bayyana cewa, hana satar amsa ne ya janyo faduwar dalibai a jarawabar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta JAMB a bana.
Tunji Alausa, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a Talatar makon nan.
Haka kuma ya ce, hakan ya nuna yadda tsarin rubuta jarabawar ya dakile satar amsa da dalibai ke yi a baya.
A ranar Litinin din makon nan ne hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da Sakandare JAMB ta fitar da sanawar cewa cikin dalibai miliyan 1 da dubu dari tara da hamsin da suka rubuta jarabawa, kimanin miliyan 1, da dubu 534 da dari 654 ne suka samu maki kasa da 200.
Haka kuma, hukumar ta ce, dalibai dubu 12 da dari 414 ne suka samu maki 300 zuwa sama.
You must be logged in to post a comment Login