Labarai
Dalibai na fuskatar kalubalen rashin karafafa gwiwa – Kungiya
Kungiyar daliban ‘yan aslin jihar Kano dake karatu a jami’ar addinin musulunci dake jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar ta ce daliban ‘yan asalin jihar nan dake karatu a can suna fuskantar kalubale ta bangaran rashin samun kwarin gwiwa daga nan gida.
Shugaban kungiyar Malam Dalha Sulaiman Ahmad ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan freedom radio wanda aka tattauana kan yadda dalibai ‘yan jihar nan dake gudanar da karatu a jihar maradi ke fuskantar matsaloli.
Ya kara da cewar duk da cewar kyauta suke gudanar da karatun a jami’ar kamata yayi daga nan gida Kano su samun goyan baya ta kowane bangare wajan kyautata karatun nasu.
Shugaban ya kuma ce ana gudanar da karatu a jami’ar kamar yadda ake gudanarwa a sauran jami’o’i a jihar nan sai yanayin yadda ake kashe kudi wajan samun gurbin karatu ne ya ban-banta.
Ana ta bangaran shugabar kungiyar da bangaran mata Khadija Sulaiman Tudun Murlata ta bayyana basa samun matsala rashin jituwa tsakanin dalibai mata da kuma malamai kamar yadda ake samu a wasu jami’o’in kasar nan.
Khadija Sulaiman kuma ta yi kira ga iyaye musamma ma mata wanda basu da dabi’ar barin yaran su karatu a wasu jami’o’i dasu basu dama shiga jami’ar addinin musulunci dake Maradi duba da cewar ta ban-banta da sauran jami’o’in kasar a wajen bada tarbiyya.
You must be logged in to post a comment Login