Labarai
Dalibai su daina tada hayaniya -KASSOSA
Kungiyar tsofaffin daliban Kwalejojin Kimiyya na jihar Kano da Jigawa KASSOSA, ta yi Allah wadai da halayyar wasu daliban Kwalejin Kimiyya ta Dawakin Tofa na tada hayaniyya tare da lalata wasu daga cikin kayan amfani na Kwalejin.
Shugaban kungiyar KASSOSA na kasa Alhaji Mustapha Nuhu Wali ne ya bayyana hakan yayin taron hadaka na dai-dai-kun kungiyoyin ajujuwan da suka kammala karatu daga Kwalejojin.
Alhaji Mustapha Nuhu Wali mni ya ce ya zama wajibi kungiyoyin ajujuwa su bada ta su gudunmawar wajen nusar da daliban Kwalejojin ta’adu na kwarai, wanda za su taimakawa daliban wajen ciyar da su gaba.
Mustapha Nuhu Wali ya kara da cewa, akwai bukatar iyaye su rinka taka rawar da ta dace, wajen baiwa ‘ya’yan su tarbiyya ingantacciyya, ta yadda za su kasance masu kaucewa irin wadannan matsaloli duk inda suka samu kansu.
Shugaban ya jaddada bukatar dake da akwai, wajen ci gaba da alkinta wadannan makarantu da shakka babu sun bada gagarumar gudunmawa wajen samar da Likitoci da Injiniyoyi da sauran Kwararru a fannoni daban-daban a fadin kasar nan.
Kungiyar KASSOSA ta gudanar da taronta na shekara a jihar Jigawa
Kungiyar KASSOSA ta jaddada kudurin ta na kawo sauyi a sha’anin karatun kimiyya
Kwalejin Kimiyya dake Dawakin Kudu ta samar da sabon dakin kwanan dalibai
Da yake bayani tun da fari, sakataren kungiyar ta KASSOSA Alhaji Hassan Abdulhamid ya bayyanawa cewa, kungiyar na yin hadin guyiwa da hukumar kimiyya da fasaha ta jihar Kano don kyautata yanayin koyo da koyarwa a Kwalejojin Kimiyyar.
Alhaji Hassan Abdulhamid Hassan ya kara da cewa, tuni kungiyar ta dauki gabarar shirya taron nusarwa akan yadda daliban Kwalejojin za su zage dantse a bangarorin karatun su, tare da kaucewa duk wani abu da ka iya kawo tasgaro a karatunsu, a wani mataki na kara tsaftace yanayin karatu tare kuma da tallafawa kokarin Gwamnati ci gaba da bada ilmi mai inganci.
You must be logged in to post a comment Login