Daliban da suka rubuta jarabawar shiga jami’a UTME na shekarar 2025 da hukumar jarabawar shiga manyan makarantun JAMB ta gudanar sun bukaci a soke sakamakon dungurungu.
Daliban sun bayyana haka ne bayan da hukumar jamb ta amsa laifin kurakurai da aka samu da suka haifar da yawan rashin kokarin daliban a jarabawar
Rashin kyauwn sakamakon Wanda sama da dalibai milliyan 1.5 suka Kasa samun maki 200 ya haifar da Cece ku ce a fadin kasar nan
Sai dai a ranar Laraba Shugaban hukumar Jamb Farfesa Ishaq Oloyede ya kira taron yan jarida inda ya amsa cewa hukumar ta gane cewa laifinta ne ya Kuma Bada hakuri kan kura kuran da aka samu a jarabawar.
You must be logged in to post a comment Login