Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar JAMB ta ce dalibai 22 sun samu matsalar daukar dan yatsa yayin rubuta jarabawar

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB ta ce dalibai 22 da suka fuskanci matsalar daukar danyatsa ta Na’ura mai kwakwalwa za su sake rubuta jarrabwar UTME a shalkwatar hukumar dake babban birnin Tarayya Abuja.

Wannan na kunshe cikin sanarwar mako-mako da hukumar JAMB ke fitarwa da ake kira da ‘’JAMBULLETIN’’ da aka fitar a ranar Lahadi a jihar Lagos cewa daliban na cikin daliabai dubu 24 da dari 490 wadanda suka fuskanci matsaalr daukar danyatsaya ta Na’ura mai kwakwalawa a yayin rubuta jarrabawar ta UTME d aka yi.

A yayin rubuta jarrabawar  daukar danyatsu guda 10 na dalibai na da  muhimmanci sosai haka kuma kafin dalibai ya shiga dakin jarrbawa sai an tantance dalibi don gudun yin magudin jarrabawa.

Kafin dai fara yin jarrabawar ta UTME tun da fari, hukumar ta JAMB ta sanar da cewar ba zata dage yin jarrabawar ba, kuma suk wani dalibi dake da matsalar daukar danyatsa sai dai ya je shalkwatar hukumar dake Abuja.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!