Labarai
Daliban Najeria na tallafawa tattalin arzikin Amurka- Cibiyar musayar dalibai
Daliban kasar nan dubu goma sha uku da dari hudu da ashirin da uku da kekaratu a kasar Amurka sun tallafawa tattalin arzikin kasar da akalla dala miliyan dari biyar da goma sha hudu a shekarar da gabata.
Rahoton wanda ke cikin wani kundin bayanai da sashen kula da harkokin ilimi na Amurka da wata cibiyar kula da harkokin musayar dalibai ta duniya suka wallafa, sun ce Najeriya kasa ce ta goma sha daya cikin kasashen waje da ke da dalibansu a kasar ta Amurka.
A cewar rahoton adadin daliban Najeriya da ke karatu a kasar ta Amurka sun kai kusan kaso daya da rabi na adadin daliban kasashen ketare da ke karatu a Amurka wanda yawansu ya kai miliyan daya da dubu casaîn da biyar da dari biyu da casa’în da tara.
Gwamnatin Kano zata sabunta tallafin ilimi na shekara 5 da kasar Faransa
Rashin kwararru a bangaren ilimi ke kawo cikas – Tajudeen Gambo
Kano zata hada kafada da kasashen duniya a bangaren ilimi –Ganduje
Kididdgar ta kuma nuna cewa daliban kasar nan dubu biyra da dari shida da tamanin da tara suna karatu a matakin digiri na farko ya yin da dubu biyar da dari biyu da sabain da hudu su ke karatun Digiri na biyu