ilimi
Daliban Sudan a Nijeriya na fargabar halin da karatunsu zai iya shiga na rashin madafa.
Dubban daliban Nijeriya ne da su ka dawo daga kasar Sudan bayan barkewar yaki a Sudan din ke cigaba da fargabar halin da karatun su zai iya shiga na tangal-tangal bayan tsaiko da suka samu, sakamakon tahowa ba shiri.
Daliban dai sun ce a yanzu haka sun bar karatun nasu ne ba tare da sanin ranar komawarsu Makarantar ba, dalilin yakin da ake gwabzawa a Sudan din, da ba ranar dainawa.
Daliban da suke ajin karshen a matakin digri din sune suka fi nuna damuwarsu, biyo bayan rashin mafitar da karatun nasu zai iya fuskanta.
Su ma iyayen wadan nan dalibai sun nuna damuwa kan zaman ‘Ya ‘yan na su a gida musamman wadanda karatun su ya yi nisa ko ma su ke shirin kammalawa.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin yawancin daliban sunje karatun ne, bayan gwamnati da dai-daikun al’umma sun dauki nauyinsu.
Hakan tasa suke kira ga gwamnati data samar musu mafita, don Kar karatun nasu ya tashi a banza.
Sai dai wata majiya mai karfi ta nuna cewa a yanzu haka gwamnati na Kan tattauna hanyar da zata bi, don ganin ta samarwa wadannan daliban da abin ya shafa mafita.
Rahoton: Alameen Sulaiman
You must be logged in to post a comment Login