Manyan Labarai
Dalilan da ke kawo tabin hankali a Kano.
An bayyana damuwa a matsayin daya daga cikin abubuwan dake jawo tabin hankali tsakanin al’ummar jahar Kano.
Babbar maaikaciyar jinya ta asibitin masu tabin hankali na Dawanau dake birnin Kano Hajiya Amina Idris ce ta bayyana hakan a cikin shirin Barka da hantsi na gidan rediyan Freedom da ya mayar da hankali game da ranar masu tabin hanakali ta Duniya .
Hajiya Amina Idris tace akwai mutane da dama bayan shaye shaye da suka samu tabin hankali saboda yawan damuwa ta rayuwar yau da kullum.
Ta bayar da misalin wani matashi da ya kammala sakandire kuma yana da kokari kwarai da gaske ,inda ya cinye duk darussan da ake bukata amma bai samu cigaba da karatu ba wanda hakan tasa ya shiga damuwa.
Amina Idris ta kara da cewa akwai wata mata da mijin ta ya saki kishiyar ta ya bar mata ‘’ya ‘’ya biyu da nata tara ,inda kullum zai bar mata naira dari biyu kacal domin ta ciyar da su,hakan yasa matar ta samu tabin hankali.
A nasa bangaren daya daga cikin bakin da ya fito daga asibitin na Dawanau Nura Idris yace masu tabin hankali suna bukatar tarairaya da jan su jiki, yace hakan na iya magance matsalar tabin hankali.