Labaran Wasanni
Dalilan da suka sa Aston Villa ta Kori mai horar da ‘yan wasan ta Gerrard
Kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa ta kori mai horas da ‘yan wasan ta, Steven Gerrard, sakamakon rashin nasara a hannun Fulham da ci 3 da nema a wasan mako na 12 a gasar Firimiyar kasar Ingila.
Wasan da ya gudana a ranar Alhamis 20 ga watan Oktoban shekarar 2022.
Gerrard mai shekaru 42 ya bar Aston Villa tana matakin ta 17 a kasan teburin gasar Firimiyar da maki Tara, bayan buga Wasanni 11 a kakar wasanni ta bana.
Aston Villa ta ci wasanni Biyu da canjaras Uku an doke ta a wasanni Shida, ta ci kwallaye Bakwai an kuma zura mata 16.
Gerrard tsohon dan wasan Liverpool an nada shi mai horas da ‘yan wasan Aston Villa ne a ranar 11 ga watan Nuwambar shekarar 2021, inda ya maye gurbin Dean Smith.
Kawo yanzu Gerrard ya ja ragamar Villa wasa 38 da cin wasanni 12 da canjaras Takwas an kuma doke shi fafatawa 18.
Haka kuma kungiyar ta ci kwallaye 45 an kuma zura mata 50 a raga karkashin jagorancin Gerrard.
You must be logged in to post a comment Login