Labarai
Dalilan da suka sanya ake tsadar kayan miya a Kano – Kungiya

Kungiyar masu sayar da kayan Gwari ta kasuwar Sharada tace matsalar tashin fashin kayan miya da ake fuskanta a wannan lokaci na da nasaba ne da karewar kayan miya na damunar data gabata.
Shugaban kungiyar masu sayar da kayan Gwari na kasuwar Sharada Alhaji Na’iya ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da wakilin Freedom Radio Abdulkarim Muhammad Tukuntawa a yau a yau
Na’iya ya kara da cewa tun da kayan miyan da aka noma na damunar da ta gabata ya fara janyewa a kasuwanni aka fara fuskantar matsalar tsadar kayan miyan a Kano.
Ya kuma kara da cewa wannan matsalar ce ta sanya tsadar da bayan da Rani bai zo kasuwa ba.
You must be logged in to post a comment Login