Labarai
Dalilan da suka sanya ake zargin Sadiya Farouq da yin rub-da-ciki da kudade
A jiya Litinin ne shugaban hukumar ICPC Farfesa Bolaji Owasanoye, ya bayyana cewar hukumar ta samu nasara a yakin da take da cin hanci da rashawa yana mai buga misali da yadda suka gano an yi rub da ciki da kudaden da aka kebe don ciyar da yara ‘yan makaranta ma su tarin yawa da ya kai sama Naira biliyan biyu.
Farfesa Bolaji Owasanoye ya bayyana hakan ne a taron da aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Amma farfesan bai ambato sunan wanda ake zargi da karkatar da wadannan kudaden ba, kasancewar yana jawabi ne kan nasarorin da hukumar ta ICPC ta samu.
Sai dai Ministar kula da harkokin jin kai da kare yaduwar ibtila’I da kasa Hajiya Sadiya Umar Farouq ta barranta kanta daga labarin da ke cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICP ta gano wasu makudan kudaden ciyar da dalibai da aka bai wa wasu kwalejoji a lokacin zaman gida da ya kai sama da biliyan biyu.
Hakan na cikin wata sanarwa ce da mai bai wa ministar shawara kan harkokin yada labarai, Nneka Anibeze ta fitar a daren jiya.
Sanarwar ta bukaci al’umma da su yi watsi da jita-jitar da ale yadawa cewa da sanin ministar aka ajiye kudaden
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, shirin ya kula da dalibai ‘yan aji daya zuwa uku ne a makarantun firamare a lokacin na dokar lockdown.
You must be logged in to post a comment Login