Labarai
Dalilan da suka sanya Buhari ya ce gwamnatoci ba zasu iya sarrafa ma’adanai ba
Gwamnatin tarayya ta ce gwamnatocin jihohin kasar nan ba zasu iya sarrafa ma’adinan da ke shimfide a jihohin su ba.
Ministan ma’adanai da bunkasa Tama da karafa, Olamilekan Adegbite, ne ya bayyana hakan a wani taron wayar da kai da ya hadar da kwamishinonin shari’a dana ma’adanai da muhalli na shiyyar Arewa ta tsakiya da suka gudanar a Abuja
Adegbite ya kuma ce ana amfani da kudaden da ake samu daga wani sashe na man fetur a kasar nan don cigaban Najeriya baki daya.
Ya kuma ce yanzu haka Najeria hankalin ta ya fara karkata ga bunkasa bangaren ma’adanai domin samar da kudaden shiga don amfanin kasar nan yadda ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login