Labarai
Dalilan da suka sanya Lauyan Abduljabbar Kabara ya nemi a sallame shi
Lauyan da yake kare Malam Abduljabbar Kabara ya roƙi kotu da ta sallami malamin.
Baya ga haka ma lauyan ya buƙaci kotun da ta umarci gwamnati ta baiwa Abduljabbar ɗin haƙuri.
A zaman kotun na ranar Alhamis ƙarƙashin jagorancin mai sharia Ibrahim Sarki Yola bayan da kotun ta ci gaba da sauraran shari’ar.
Tun da fari Lauyan gwamnati Barista Yakubu Abdullahi ya gabatar da kansa tare da mataimakansa haka shi ma Lauyan wanda ake ƙara Barista Dalhatu Shehu ya gabatar da kansa.
Bayan haka ne kuma Lauyan gwamnati ta bakin Barista Abdurrahman Mukhtar ya fara yiwa malamin tambayoyi kamar haka.
“Wannan ƙur’anin da muke amfani da shi cikakkene”?
Sai malam Abduljabbar ya ce “kwarai kuwa“.
Sai ya sake yi masa tambayar cewa “menene matsayin karatunka“?
A anan ne aka dinga mai Ruwa rana daga ƙarshe malamin yace “ina da digirin digirgir wanda na samu daga haɗakar wata jami’ar Amurka da ke Ghana”.
Haka kuma an yi masa tambayar Ijaza wato kwalin da ke tabbatar da sahihancin iliminsa nan ma Abduljabbar Kabara ya ce “akwai na gidanmu da na mallaka da kuma wani malami da ya bani a Morroco”.
Daga ƙarshe Lauyan gwamnati ya yi Masa tambaya a kan cewar ko yana da wata aƙida ta cewar Alkurani ba cikakke bane? a nan ne malamin ya musanta har ma ya ce “ni dai na bada bayani ne daga cikin wasu littatafai“.
Bayan kammala tambayoyin ne sai Lauyan Malam Abduljabbar ya tashi ya ce yana da magana tare da rokar kotun da ta sallami malamin bisa hujjar da ya dogara cewa bayanan da ake zargin Abduljabbar ɗin da su ba su inganta ba.
A don haka ya buƙaci kotun ta sallami malamin ta kuma umarci gwamnati ta bashi haƙuri da kuma neman afuwarsa.
Nan take Lauyan gwamnati ya yi suka kan buƙatar hakan, inda ya ce ai wannan riga Malam masallaci ne kawai saboda babu mahallin buƙatar hakan a cikin sashi na 390(2) amma yana da damar ƙalubalantar cajin kafin yanke hukunci.
Daga haka ne kuma kotun ta dage zamanta zuwa ranar 7/7/2022 domin fadar ra’ayinta kan yiwuwar sallamarsa ko akasin haka, kamar yadda wakilin Freedom Radio Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito mana.
You must be logged in to post a comment Login