Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kamata ya yi Buhari ya tura dakarun kasar nan Amurka – Masani

Published

on

Wani malami a Tsangayar nazarin harkokin tarihi da al’amuran kasa da kasa na Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke nan Kano Malam Kabiru Ibrahim Danguguwa, ya ce kamata ya yi gwamnatin tarayya ta tura dakarun tsaron kasar nan Amurka domin samun horo na musamman, maimakon neman daukin Amurkar kan yaki da ta’addanci.

Malam Kabiru Ibrahim Danguguwa ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da wakilinmu Auwal Hassan Fagge kan yadda shugabannin Afirka ke neman daukin kasashen Turai.

Kabiru Danguguwa ya ce akwai kasashe da dama da kasar ta Amurka ta kaiwa daukin yaki da ta’addanci, amma hakan bai sa an samu nasara ba.

Malam Kabiru Ibrahim Danguguwa, ya kara da cewa sai dai Najeriya za ta iya neman shawarar kasar a harkar bunkasa tattalin arziki ta fuskar neman shawarwari, ko kuma bukatar kasar ta zuba jari a tattalin arzikinta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!