Labarai
Dambarwar Mahadi Shehu ci gaba ne a siyasar Katsina – Masana
A jihar Katsina ana ci gaba da dambarwa kan zarge-zargen da Mahadi Shehu ya yi wa gwamnatin jihar, na karkatar da akalar wasu makudan kudaden gwamnati, inda batun ke ci gaba da zama maudu’in tattaunawa a jihar.
Kusan makonni uku kenan, wannan batu na ci gaba da daukar hankali, a wuraren zama da haduwar jama’a a jihar ta Katsina.
Wasu ‘yan jihar ta Katsina da Freedom Radio ta zanta da su sun bayyana mana mabam-bamtan ra’ayoyi kan wannan dambarwa.
Yayin da wasu ke kalubalantar gwamnati kan yakamata ta dauki matakin shari’a akan sa, domin tabbatar da gaskiyar al’amari.
Wa su kuwa na cewa, Mahadin ya nemi afuwar gwamnati, tunda gwamnatin jihar ta musanta zarge-zargen.
Dakta Kabir Umar ‘Yan Daki malami a sashen kimiyyar siyasa na jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua dake Katsina, ya ce, ci gaba aka samu a siyasar jihar Katsina.
“na daya dai a duk jihohin Najeriya, ina ganin babu jihar da aka samu ci gaba kamar haka, yana daya daga cikin ginshikai na dimokuradiyya cewar su talakawa su san yaya a ke yi da kudin su, to ni ina ganin wannan abin ci gaba ne gaskiya, an samu ci gaba” inji Dakta Kabir ‘Yan Daki.
You must be logged in to post a comment Login