Labaran Kano
Dan Hisbah yayi karar hukumar Hisbah a Kano
Wani jami’in Hisbah mai suna Bashir Ja’afar ya shigar da karar hukumar Hisbah ta jihar Kano a gaban hukumar karbar korafe-korafe ta Kano wato Anti Corruption.
Bashir Ja’afar na zargin cewa hukumar Hisbah ta tauye masa hakki, a yayin jarrabawar sabbin kwamandojin hukumar na kananan hukumomi.
Hukumar Hisbah dai ta kafa kwamitin tantancewa da jarrabawa ga Kwamandojin kananan hukumomi karkashin tsohon babban kwamandan hukumar Malam Ibrahim Mu’azzam Maibushra.
A sakamakon tantancewar ne Bashir Ja’afar daga karamar hukumar Madobi ya samu maki 81 da digo 6 cikin dari, yayin da mai biye masa kuma Abdurrazak Imam ya samu maki 66 da digo 12 cikin dari.
Amma sai hukumomin Hisbah suka sanya Abdurrazak Imam matsayin kwamanda shi kuma Bashir Ja’afar aka ce ya karbi mataimaki.
Wasu rahotonni na cewa wani babban dan siyasa a karamar hukumar Madobi shi ne ya bada zabinsa cewa lallai Hisbah ta nada Abdurrazak Imam.
Wakilinmu Yusuf Ali Abdallah ya garzaya hukumar Hisbah inda ya samu tattaunawa da Dakta Aliyu Musa Aliyu Kibiya babban daraktan hukumar Hisbah wanda ake zargin shi ne ke da ruwa wajen yin wannan sauyi, sai dai ya shaida mana cewa Bashir Ja’afar dake korafi kukan dadi yake, domin kuwa alfarma suka yi masa, kasancewar baya cikin ‘yan takarar kwamandoji na kananan hukumomi.
Shin dama ana iya baiwa sojan gona mukamin mataimaki?
Sai Babban darakta ya ce taimako ne, don gudun kada yayi biyu babu.
Shugaban hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado ya tabbatarwa da Freedom Radio cewa tuni suka karbi wannan korafin, kuma zasu gayyaci hukumar Hisbah domin fadada bincike akai.
Labarai masu alaka:
Hukumar Hisbah ta Kano ta cimma yarjejeniyar aiki da KAROTA
Hisbah zata bude sabbin ofisoshi a Kano