Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Yadda hukumar Hisbah ta sauke ‘yan kwamitin gudanarwarta

Published

on

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sauke ‘yan kwamitin gudanarwa na hukumar na kananan hukumomi 44 dake Kano.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin babban kwamandan Hisbah Shaikh Harun Muhammad Ibn Sina inda ya sanar da sauke daukacin yan kwamitin daga kan matsayi da kuma mukamansu sakamakon wasu gyare-gyare da akeyi a hukumar.
Sai dai Sheikh Ibn Sina ya ce har yanzu suna nan a mastayinsu na ‘yan Hisbah wato dai mukamai da matsayin da suke kai ne kawai aka cire.

Tuni dai hukumar Hisbah ta jihar Kano ta baiwa kwamandojin kananan hukumomi kwanaki 8 kan su kawo sunayen mutum takwas – takwas wadanda za a tantance a zabi mutum 4 daga ciki, bi sharadin dole ne su zama daga cikin yan Hisbah, kuma wajibine duk wanda za’a kawo ya kasance ya samu akalla shekara biyar yana aikin Hisbah.

Sannan dan 30 zuwa 60, tuni aka kaddamar da kwamitin da zai yi aikin tantance wadannan mukamai, haka kuma babban kwamanda ya sanar da rushe kwamitocin bada shawara na Hisbah banda masu Kujeru na dindindin wadanda suka hadar da Hakimi, Babban Limamin gari da DPO da sauran masu ruwa da tsaki.

RUBUTU MASU ALAKA:

Dan Hisba ya ki karbar rashawa

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata kwalaben barasa 196,400

Gwamnatin Kano zata samar da Sabuwar shelkwatar hukumar Hisbah ta bayar da horo na musaman

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!