Labaran Kano
Dan jihar Kano ya zama shugaban shiyya na SDGs
Gwamnatin tarayya ta nada mai baiwa gwamnan Kano shawara dorewar cigaban karni Habibu Yahya Hotoro a matsayin shugaban shirin na shiyyar Arewa maso yamma.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Gwamnan Kano Abba Anwar ya fitar a jiya Alhamis.
Sanarwar ta ce nadin Habibu Yahya Hotoro na cikin wata takarda dauke da sanya hannun hadin gwiwa na mataimakiyar shugaban shirin Misis J. Adebimpe Aor da kuma shugaban shirin dorewar cigaban karni Dr. M. A. Ibrahim.
A cewar sanarwar, shugabancin Arewa maso yamma ya hada da jihohin Kano da Jigawa da Kaduna da Katsina Sokoto da Kebbi da kuma Zamfara, don bunkasa yanayin aikin na dorewa cigaban muradun karni a shiyyar.
Nadin dai ya biyo bayan zaman da shugabanni jihohi 36 suak yi da kuma amincewar ofishin mai taimaka shugaban kasa na musamman kan dorewar cigaban muradan karni.
Sanarwar ta kara da cewa, shakka babu nadin zai baiwa sabon shugaban kwarin gwiwa, da kuma fito da sababbin manufofin shirin na dorewar cigaban al’umma.
Idan ba a manta ba dai, a makwannin baya ne Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada Habibu Yahya Hotoro a matsayin mai bashi shawara akan ci gaban karni, biyo bayan kwarewa da yake da ita a bangaren ciyar da al’umma gaba.
Habib Yahya Hotoro yana da Digiri na farko dana biyu a fannin shari’a.