Kiwon Lafiya
Dan majalisar mai wakilya mazabar Pengana a jihar Filato ya mutu
Dan majalisar dokoki mai wakiltar mazabar Pengana a jihar Filato daga jam’iyyar APC mai mulki Ezekiel Afon ya mutu.
Sakataren jam’iyyar APC na jihar ta Filato Bashir Sati ya tabbatar da rasuwar marigayin Ezekiel Afon a tattaunawar sa da manema labarai a Jos babban birnin jihar ta Filato.
A cewar rahoton Mr Afon shi ne ya sake lashe zaben majalisar dokoki jim kadan bayan sanar da cewa shi ne ya lashe zaben mazabar sa, kasancewar yana fama da rashin lafiyar aka dauke shi zuwa a wani asibiti dake kasashen waje, amma kuma jim kadan da sanar da cewa ya lashe zaben aka bayyana cewar ya rasu a jiya Lahadi.
Sakataren jam’iyyar APC ya ce ya kado matuka da rasuwar marigayin, bayan da jam’iyyar APC ke tsaka da gudanar da murnar sake lashe zaben sa. An dai zabe Mr Ezekiel Afon a shekara ta 2015 a karkashin jam’iyyar PDP, sai dai daga baya ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai ci ta APC yayin da aka sake zabar a ranar Asabar a mazabar ta Pengana