Labarai
Dan tsami ya janyo mana rashin ciniki – Masu sana’ar sayar da lamurje a Kano
Masu sana’ar sayar da lemeon lamurje sun yi korafin cewa suna fama da rashin ciniki wanda suka alakanta hakan da batun dan tsami da hukumomi suka ce ya yi sanadiyar wasu mutane sun rasa rayukansu a Kano a kwanakin baya.
A cewar mutanen tun bayan da aka yi zargin cewa sinadarin dan tsami ne ya janyo wasu mutane suka mutu sannan wasu da dama suke karbar magani a asibiti, suka fara ganin koma baya a cinikinsu.
Malam Awwalu Nagarta flavor daya ne daga cikin masu sana’ar sayar da kayan hadin lemon a kasuwar Rimi da ke Kano, shima cewa ya yi, ko da su da suke sayar da kayan hadin lemon sun shiga mawuyacin hali sanadiyar rashin ciniki da suke fama da shi a wannan lokaci.
‘‘Sanin kowane babu lokacin da sana’ar mu ta fi garawa kamar lokacin azumi amma a bana lamarin ya canja’’ a cewar sa.
Ya kuma godewa gwamnati sakamakon yadda ya ce ta shigo don tsaface sana’ar tasu ta hanyar fitar da baragurbi da ke gurbata sana’ar ta su da kayayyaki marasa inganci.
You must be logged in to post a comment Login