Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Burinmu mu zama na goma a duniyar kwallon kwando- Akhator

Published

on

‘Yar wasan kungiyar kwallon Kwando ta kasa ta mata D’Tigress Evelyn Akhator, ta ce buga gasar wasannin motsa jiki na bazara wato Olympic shi ne babban burinta, tun bayan da ta fara wakiltar kungiyar a matsayin ‘yar wasa.

Akhator, ta kara da cewa burin tawagar ‘yan wasan kungiyar ne dukkan su na ganin cewar kungiyar ta zama tana daga cikin kungiyoyi goma mafi hazaka na duniya.

“Burin kowanne dan wasa ne zuwa gasar Olympic, don haka ne ma da munji an ambaci sunan Olympic, sai mu kara jin wani karsashi na musamman, wanda zuwa yanzu haka fatan mu shine aganin shekarar badi mai zuwa don wakiltar kasar mu, inji ‘yar wasan”.

Labarai masu alaka.

Tennis: Venus da Serena Williams da Sloane Stephens basu ne bakar fataba kawai

Hukumar NBBF za ta cigaba da gudanar da gasar kwallon Kwando duk da kai ta kara da aka yi

Akhator , ta kara dacewa  a baya ba wanda ya yarda cewar zamu zama daya daga cikin kasashe 20, dake kan gaba a duniyar  kwallon Kwando ta mata, sai gashi yanzu muna mataki na 14, wanda ba karamin cigaba bane duba da cewa kwallon Kwando a kasar nan bata kai yadda take da farin jini a kasar Senegal ba.

Hakan na da matukar muhimmanci kwarai da gaske, ya kuma fito da sunan kasar nan a idon duniya wajen kwallon Kwando ta duniya

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!