Labaran Wasanni
Dan wasan Super Eagles Paul Onuachu ya lashe takalmin zinare
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Paul Onuachu, ya lashe takalmin zinare na shekarar 2021 a kasar Belgium.
Onuachu ya zama na farko a Najeriya kuma na hudu a nahiyar afrika da ya lashe kyautar.
Dan wasan tawagar Najeriya yabi sahun ‘yan wasa Aruna Dindane na kasar Cote d’Ivoire da ya lashe a shekarar (2003) da dan wasan Morocco’s Mbark Boussoufa da ya lashe har sau biyu a (2006 da 2010) sai kuma dan wasan kasar jamhuriyar DR Congo’s Dieumerci Mbokani wanda ya lashe (2012)
Kyautar takalmin zinare din dai ana bayar da ita ne a ko wacce shekara ga dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a gasar.
Onuachu ya doke takwarorinsa bayan samun kuri’i 333, inda dan wasan Club Brugge Noa Lang ya samu kuri’a (272 votes) sai Charles De Ketelaere da ya samu (271 wanda hakan ya basu damar kasancewa na biyu da kuma na uku.
Mai shekarau 27 a kakar wasannin da ta gabata ya kammala a mataki na uku a bayan ‘yan wasa Lior Refaelov da Raphael Holzhauser.
Sai dai a bana ya kammala a na farko da yawan kwallaye
29 a kakar wasannin 2020-21, inda kuma a yanzu ya zura kwallaye 12 a rabin kakar wasannin da muke ciki.
Kuma wannan nasarar da ya samu ya sa Onuachu zama na uku a tarihin Genk da ya lashe a tsahon shekaru 20 da suka gabata.
Onuachu baya cikin ‘yan wasan Super Eagles da suke fafatawa a gasar AFCON da ke fafatawa a kasar Kamaru sakamakon raunin da ya ji.
You must be logged in to post a comment Login