Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Darajar Rai: An ƙone ɓarawon babur a Wudil

Published

on

Wasu fusatattun matasa sun hallaka wani matashi har lahira ta hanyar ƙona shi da taya a garin Wudil da ke jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a jiya Litinin bayan da aka zargi matashin da satar babur a ƙofar bankin Zenith da ke Wudil.

Fusatattun matasan sun bi bayan sa tare da yi masa ihun ɓarawo-ɓarawo yayin da ya nufi Garin-Dau da ke ƙaramar hukumar Warawa.

Shugaban ƴan sintiri na jihar Kano Muhammad Kabiru Alhaji ya ce, sun yi iya ƙoƙarin su domin su ceci ransa amma lamarin ya ci tura.

‘‘Jami’an mu sun yi iya kokarinsu wajen ceto shi daga hannun matasa don mika shi gaban kuliya amma lamarin ya ci tura’’ a cewar MK Alhaji.

Muhammad Kabiru Alhaji ya kuma ce, tuni suka miƙa gawar mamacin ga ƴan sanda.

‘‘A bangare guda mun kuma kama wasu matasa da ake zarginsu da satar Awakai’’ inji shugaban kungiyar ‘yan sintirin na Vigilante.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!