Labarai
Dattijan Kano sun nemi Buhari ya ki amincewa da bukatar Ganduje
Wasu dattawan jihar Kano ‘yan kungiyar Kano Unity Forum sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da majalisun dokokin tarayya da kuma ma’aikatar kudi ta tarayya da su ki amincewa da bashin da gwamnatin Kano ke neman karbowa daga kasar China don aikin jirgin kasa da ya kai naira biliyan dari uku.
Kungiyar ta Kano Unity Forum karkashin jagorancin Alhaji Bashir Tofa ta bayyana adawarta karara da ciyo bashin daga China Development bank don shimfida layin dogo a birnin Kano.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Alhaji Bashir Tofa a madadin kungiyar ta Kano Unity Forum aka kuma rabawa manema labarai a yau Alhamis, ta ce abin damuwar babu wanda ya san ka’idojin da ke cikin yarjejeniyar kafin ba da bashin.
Kungiyar ta Kano Unity Forum ta ce indai har kasar China ta na son taimakawa jihar Kano ce da to ba wai a bangaren shimfida layin dogo za ta kawo dauki kamata yayi ta kawo dauki ta bangaren ilimi da lafiya da aikin gona da samar da wutar lantarki da masana’antu, samar da ruwan sha da kuma kimiyya da fasaha.
You must be logged in to post a comment Login