Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Daurarru sun bukaci daukin shugaba Tinubu

Published

on

Wasu daurarru da ke zaman jiran shari’a a gidan gyaran hali na Kaduna, sun bukaci shugaba Tinubu da majalisun tarayya da su samar da dokar magance jimawa ana zaman jiran shari’a kamar yadda tsarin ya ke a wasu manyan kasashen duniya.

Daurarrun, sun bayyana hakan ne yayin da kungiyar Ansar-ud-deen shiyyar Kaduna ta kai ziyara gidan gyaran hali a jihar, inda suka bayyana cewa, suna tsare na tsawon watanni har ma wasu daga cikinsu an daina yin shari’ar su.

A nasa jawabin, babban Limamin masallacin Ansar-ud-deen na Kaduna Alhaji AbdulAzeez Kijan, wanda ya jagoranci kai ziyarar, kimanin daurarru 1,273 cikin 1,669 wadanda ke tsare a gidan duk masu jiran shari’a ne.

Haka kuma ya ce, daurarru 1,233 cikin 1,626 maza ne yayin da yayin da 40 daga cikin mata 47 da ke tsare duk masu jiran shari’a ne, inda ya kuma bayyana cewa kuma haka abub ya ke a sauran gidajen gyaran halin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!