Labaran Kano
Fiye da Daurraru 1,000 sun amfana da duba lafiyarsu daga likitoci
Daurraru sama da dubu daya ne dake gidajen gyaran hali na Goron Dutse da na Kurmawa a jihar Kano sun amfana da ganin likitoci daban-daban tare da ba su magunguna kyauta.
Yayin wani aikin sa-kai da tawagar kungiyar likitoci musulmi suka yi karkashin jagarancin shugaban kwamitin gudanar da aikin Dakta Sule Abdullahi Gaya.
Shugaban kungiyar a jihar Kano Dakta Muhammad Auwal, ya ce, suna yin aikin ne domin taimaka wa marasa karfi a wurare daban-daban, tare da basu kayan abinci da ruwa kyauta.
A nasu bangaren wasu daga cikin likitocin da suka duba marasa lafiya a gidan gyran hali da suka hadar da Dakta Anas Ibrahim Yahaya Bichi da Dakta Muhammad Lawan Adamu, cewa suka yi a tafiyar ta su babu irin likitan da babu, don haka kowacce irin cuta suka ci karo da ita sun tanadi maganin ta.
Daga bisani mai kula da gidan gyaran halin na Kurmawa DC Mu’azu Tukur wanda ya yi jawabi a madadin shugaban hukumar ya nuna godiya da jin dadin kan aikin da kungiyar likitoci musulmi suka yi ga daurarrun.
You must be logged in to post a comment Login