Labarai
Daurawa ya ajiye mukaminsa na shugaban Hisba
A yau juma’a ne 10 ga watan Mayu 2019 shugaban hukumar HISBA ta jihar Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya mika takardar ajiye aiki daga shugabantar hukumar ga gwamnatin jihar Kano.
Takardar ajiye aikin wadda hadimin Sheikh Ibrahim Daurawa din, Malam Umar Muhammad Tukur ya mika takardar ajiye aikin a ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano.
Malam Umar Muhammad Tukur ya bayyana cewa ya kuma mika takardar Sheikh Daurawa din tare da wasu malamai uku da ke rike da mukamai daban-daban a gwamnatin ta jihar Kano.
Malaman kuwa su ne Malam Abba Koki, shugaban hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano da Malam Abubakar Umar Kandahar da Malam Nazifi Inuwa.
Koda yake Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya ce ya ajiye aikin ne bisa radin kansa, shi kuwa Malam Abba Koki cewa ya yi dalilan rashin lafiya ne ya sanya shi sauka daga mukamin nasa.
Daga bisani Malam Aminu Daurawa ya yi bayani a shafin sada zumunta na ‘facebook’, inda ya sanar da cewa shi da abokansa su 4 sun sauka daga mukamansu saboda wasu dalilai da sai nan gaba ne za su bayyana.
Ita kuwa gwamnatin jihar Kano ta bakin kwamashinan yada Labarai, Malam Mohammed Garba cewa ta yi dama tuni gwamna Ganduje ya umarci dukkan masu rike da mukamai a gwamnatin su shirya barin aiki saboda shirin shiga wa’adi na biyu da za a yi a karshen wannan watan.